Home Kasashen Ketare Manoma za suyi taron karawa juna sani a Dubai

Manoma za suyi taron karawa juna sani a Dubai

61
0

Daga Hannatu Mani Abu

Taron wanda kungiyar lead consultant crenov8 ta shirya na da nufin tattara manoma a duk fadin duniya domin nemo hanyoyin bunkasa harkar noma da huddatayya tsakanin manoma da masu sayan amfanin gona.

Wasu manoman Nijeriya a bakin aiki

Bola Oyedele, yar Nijeriya na daya daga cikin masu shirye shiryen gudanar da taron, ta kuma bayyana wa manema labaru cewa masu ruwa da tsaki a duk fadin Afrika da wata hukuma a yankin tekun Gulf mai suna GCC za su tattauna muhimman batutuwa akan sabbin hanyoyin habbaka kasuwanci.

Bola ta kara da cewa daukacin manoman Afrika da ma sauran mahalarta taron za su samu damar samun jari a kasar ta Dubai domin bunkasa kasuwancin su.

Manoma a gonar masara

Mahalarta taron za su kara fahimtar muhimman fannoni da su ka hada da abubuwan da ake bukata wajen fita da shigo da kaya daga kasashen ketare tare da dokokin da suka jibanci biyan kudi da dakon kaya a jiragen ruwa.

Bola ta ce muna farin ciki sosai kasancewar Afrika na cikin wadanda za su halarci wannan taron da ake sa ran zai kawo gagarumin canji a harkar noman abinci da kasuwanci tare da kara kyakkyawar alaka tsakanin Afrika da sauran kasashen duniya akan harkar noma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply