Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta yi asarar kudin da suka kai darajar Naira bilyan 1 ta dalilin ambaliyar ruwa a daminar bana a sassa daban-daban da ya yi sanadiyyar lalacewar shinkafa da sauran kayan gona a jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma roki gwamnatin tarayya da ta gina madatsar ruwa don kauce wa ambaliyar ruwa a jihar.
Kwamishinan aikin gona na jihar Attahiru Maccido ya bayyana haka a lokacin ziyarar gani da ido a wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa a kananan hukumomin Argungu da Bagudo na jihar.
Attahiru ya ce ambaliyar ruwan ta hadiye kadada dubbai na gonaki, sannan ta lalata gidaje da kayan abinci masu dama a yankunan jihar daban-daban.
