Akalla mutane 55 ne suka warke daga cutar Covid-19 a kasar Madagascar bayan sun yi amfani da maganin da kasar ta samar.
Yawan wadanda suka warken bayan sun yi amfani da maganin ya karu ne bayan sanarwar karin wasu uku da suka warke a ranar Asabar.
Marasa lafiyar na daga cikin wadanda aka yiwa amfani da maganin tun bayan kaddamar da shi a watan Afirilu.
Gwamnatin kasar ta ce tana bayar da maganin ne kyauta ga jama’ar kasar, domin taimakawa wajen magance cutar a kasar.
