Tottenham Hotspur ta cimma yarjejeniya da Manchester City kan daukar dan wasan gaba na Masar, Omar Marmoush, a matsayin aro, tare da sharadin da zai ba ta damar sayensa na dindindin kan fam miliyan 60 a bazara mai zuwa.
Jaridar Punch, wadda ta nakalto rahoton BBC Sport, ta ce dan wasan mai shekaru 27 zai koma Tottenham ne bayan ya kasa samun damar buga wasanni akai-akai tun bayan komawarsa Manchester City daga Eintracht Frankfurt.
Marmoush ya koma Manchester City a watan Janairun 2025 kan fam miliyan 59, bayan ya yi fice a gasar Bundesliga ta Jamus. Sai dai kasancewar Erling Haaland a kungiyar ya rage masa damar kasancewa cikin ’yan wasan farko.
Marmoush ya buga wasanni 62 a dukkan wasar da ya yi tun bayan komawarsa City, inda ya zura kwallaye 16. A kakar 2025/26 kuwa, ya buga wasanni 36, ya ci kwallaye takwas, yayin da a gasar Premier League ya fara wasanni takwas kacal, inda ya samu mintuna kusan 700 tare da kwallaye uku da taimakon kwallaye uku.
Komawarsa Tottenham na iya ba dan wasan damar samun karin lokacin wasa da kuma farfado da bajintarsa. Kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, zai iya amfani da kwarewar Marmoush ta taka leda a matsayin dan wasan gaba, ko daga gefe, ko kuma a bayan dan wasan gaba.
Tottenham ta kashe makudan kudade a kasuwar saye da sayar da ’yan wasa ta bazara, inda rahotanni suka ce kudin da ta kashe ya haura fam miliyan 312. Idan aka kammala cinikin Marmoush kan fam miliyan 60, zai zama wani babban karin karfi ga kungiyar da ke kokarin inganta bangaren kai hari.
