Home Sabon Labari Martani bayan da Sanata Ekweremadu ya sha da ƙyar a hannun ƴan...

Martani bayan da Sanata Ekweremadu ya sha da ƙyar a hannun ƴan Biafra

180
0

Daga Nuruddeen Ishaq Banye

Tuni dai kungiyar Ohanaeze Ndigbo da ta kun shi dattijan kabilar Igbo a Nijeriya ta yi Ala-Wadai da yunkurin keta wa Ike Ekweremadu rigar mutumci a bainar jama’a.

Gwammnatin Nijeriya ma a tabakin Hon Abike Dabiri-Erewa shugabar hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje ta nuna fushin ta a kan wannan yunkurin. Gwamnatin ta ce abin da aka so aikatawa Mr Ekweremadu abu ne da ya zubar da mutumcin Nijeriya a idon diuniya.

Hoton Ekweremadu a hannun matasan Igbo

A jiya Asabar ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ta Nijeriyar ya ci karo da fushin wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne da ke rajin tabbatar da ƙasar Biafra.

Al’amarin dai ya faru ne a birnin Nuremberg da ke tarayyar Jamus, inda waɗanda ake zargin suka riƙa jifar sa a lokacin wani taro.

An dai fitar da Ekweremadu daga wurin ne cikin wata mota, a daidai lokacin da masu jefar sa, ke ƙoƙarin hana a fice da shi daga wurin.

Jaridar DCL Hausa ta kalli wani faifan bidiyo wanda a cikinsa aka nuna wasu ‘yan kabilar Igbo su na zagi da nushin dan majalisar Nijeriyar, har dai daga karshe da alama ya sha da kyar. Amma bidiyon ya nuna karara yadda aka yaga wa dan majlisar riga.

Ike Ekweremadu Sanatan da aka aika wa hari

Da yake faɗin yadda abun ya kasance, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, ya ce ya je wurin ne domin halartar taron baje kolin al’adun ƙabilar Igbo wanda aka gayyace su shi da shugaban ƙabilar mazauna Jamus Chief Nnia Nwodo wanda bai samu damar zuwa ba.

Ya ce komai na tafiya daidai a taron, kafin wasu da suke iƙirarin ƴan IPOB ne su zo su tarwatsa taron, akan abun da suka fake da shi na ba wani taron da za a yi, a daidai lokacin da ake kashe mutane a yankin nasu.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply