Home Labarai Maryam Booth ta bayyana wanda ya fitar da bidiyon tsiraicin ta, ta...

Maryam Booth ta bayyana wanda ya fitar da bidiyon tsiraicin ta, ta yi barazanar kai shi kotu

81
0

Shahararriyar ‘yar wasan nan Maryam Booth ta magantu kan wani faifan bidiyo da ya bulla a kafafen sadarwa na zamani da aka dauke ta tsirara.

An nuna jarumar mai shekaru 26 tsirara ne a bidiyon mai tsawon dakika 2, wanda ake zargin wani tsohon saurayin ta ne ya fitar da shi.

A wani rubutu da ta yi kan batun da daren jiya a shafin tan a Twitter, Maryam ta tabbatar da cewa wani saurayin ta ne Ibrahim Ahmad Rufai da aka fi sani da Deezell ya fitar da bidiyon.

Ta ce tsohon saurayin nata ya sha yi mata barazanar zai fitar da faifan bidiyon idan har bata bashi kudi.

Da take tabbatar da cewa ita ce a faifan bidiyon, Booth, ta ce tsohon saurayin nata ya dauke ta ne a sace, lokacin da take sauya kaya, kimannin shekaru uku da suka gabata.

jarumar ta kuma yi barazanar daukar matakin shari’a a kan sa, inda ta ce tana jiran jami’an tsaro da ke gudanar da binciken su a halin yanzu tare da shawarwarin da take samu daga ‘yan uwan ta.

A cikin bayanin nata, ta godewa ‘yan uwa, abokan arziki da kuma masoyan ta, kan sakonnin jajantawa da kwarin gwiwa da suke aiko mata.

karanta cikakken bayanin nata a nan

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply