Home Labarai Masari ya hana fara tallata ƴan takarar 2023

Masari ya hana fara tallata ƴan takarar 2023

176
0

Gwamnan jihar Katsina ya ja kunnen masu tallata duk wani dantakara a jihar a halin da ake ciki.

Gwamna Masari na magana ne a taron shugabannin jam’iyyar APC na jihar da aka kira a Katsina.

Yace duka-duka shekara daya da ‘yan kwanaki da hawan gwamnatin a karo na biyu, ” don haka babu wani dalilin fara tallar wani dantakara tun daga dan majalisar jiha har ya zuwa shugaban kasa”.

Alhaji Aminu Masari ya kara da cewa ba ‘yan siyasa ba, ko da ma’aikacin gwamnati ne aka samu yana tallata dantakara, to kuwa shakka babu , zai iya samun matsala a wajen aikinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply