Home Coronavirus Masu Corona a Kano sun kai 115

Masu Corona a Kano sun kai 115

95
0
Hukumar kula da takaita yaduwar cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta ce kawo karfe 11.50 PM na ranar Talata jihar Kano na da mutum 115 masu Covid-19.
 
Sabbin kamu guda 38 da jihar ta samu a ranar Talata ne suka kai adadin masu cutar ya kai 115.
 
Jihar Borno ke take ma jihar Kano baya a arewacin Nijeriya inda Borno din take da mutane 53 yayin da jihar Gombe ke da 46, jihar Katsina kuma mutum 30.
 
A Nijeriya dai gaba daya mutum 1532 suka kamu da Covid-19. A cikin wannan adadi 44 sun mutu 255 kuma sun warke.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply