Home Coronavirus Masu Corona a Katsina sun kai 21

Masu Corona a Katsina sun kai 21

89
0

Hukumar kula da takaita yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta sanar da cewa a yanzu an samu karin mutum biyar da sakamako ya nuna suna da coronavirus a jihar Katsina wanda ya kawo adadin zuwa 21 a fadin jihar gaba daya.

Jihar dai ta sanar da rufe kananan hukumomin Mashi da Jibia don takaita yaduwar cutar bayan da aka bayar da labarin bullar cutar. Jihar kuma yanzu ita ce jiha ta hudu a jerin jihohin da ke da cutar a Nijeriya.

Kawo karfe 11.25 na dare a ranar Laraba ga adadin masu corona a Nijeriya:

Lagos-504

FCT-119

Kano-73

Ogun-24

Katsina-21

Osun-20

Oyo-17

Edo-17

Kwara-10

Kaduna-9

Akwa Ibom-9

Borno-9

Bauchi-8

Delta-6

Gombe-5

Ekiti-4

Ondo-3

Rivers-3

Jigawa-2

Enugu-2

Niger-2

Abia-2

Benue-1

Anambra-1

Sokoto-1

Adamawa-1

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply