Home Coronavirus Masu coronavirus a Legas na tserewa daga wurin killace su

Masu coronavirus a Legas na tserewa daga wurin killace su

213
0

Kwamisinan lafiya na jihar Legas ya yi korafin wadanda aka gano sun harbu da kwaronairos na ta tserewa, kuma nan da watan Yuli na wannan shekarar wadanda za su harbu a jihar za su kai mutum dubu dari da ashirin. Gwamnatin jihar ta amince a soma gwajin kulorakwin wajen warkar da masu lalurar cutar a jihar daga makon gobe.

A gefe guda kuma rahotanni sun ce Gwamnan jihar ta Legas Mr. Babajide Sanwo-Olu ya mika kanshi a karo na uku domin a yi masa gwajin cutar coronavirus. Wannan ya biyo bayan yadda aka samu wasu daga cikin ma’aikatan da ke aiki a gidan gwamnati da cutar mai saurin yaduwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply