A Alhamis din nan wasu mutane da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne suka kashe Oba Adeusi sarki mai daraja ta daya a jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya.
An sace Oba Adeusi ne lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Akure, babban birnin jihar, inda ya halarci taron majalisar sarakunan gargajiya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Tee Leo-Ikoro, ya tabbatar da faruwar lamarin. Leo-Ikoro ya ce masu garkuwar sun kuma yi garkuwa da mutane biyu daga cikin ayarin Oba Adeusi bayan sun hallakashi. Ikoro ya kara da cewa tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bolaji Salami, ya umurci jami’an ‘yan sanda na yankin da su dukufa aiki don ganin sun gano wadannan bata gari.
