Home Labarai Masu garkuwa sun sake sace matan aure uku da yara a Zamfara

Masu garkuwa sun sake sace matan aure uku da yara a Zamfara

193
0

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari gidan wani Ibrahim Abubakar da ke kauyen Dareta a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, tare da tafiya da matansa uku, yara da wani mazaunin gidan.

Shaidun gani da ido sun ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe 1:00am na daren Laraba, lokacin da masu garkuwar suka shigo kauyen, kuma suka fara harbin bindiga ba kakkautawa, saidai ba su hari kowa ba.

Wannan dai na zuwa ne kusan kwana guda, bayan wasu masu garkuwa sun shiga gidan tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Zamfara Alhaji Bello Dankande Gamji suka tafi da yaransa biyu da jami’an tsaron Civil Defense guda biyu.

Solacebase ta ruwaito cewa, kokarin jin tabikin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammad Shehu ya ci tura saboda rashin samun sa ta waya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply