Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Masu lambar NIN suna da damar dawo da tsaffin layukansu – ALTO

Masu lambar NIN suna da damar dawo da tsaffin layukansu – ALTO

160
0

Kungiyar kamfanonin sadarwar Nijeriya ta bada sanarwar cewa daga yanzu duk mai lambar shedar zama dan kasa, za su iya dawo da tsaffin layukansu da suka lalace ko suka bace a dukkan cibiyoyin kula da abokan huldar kamfanonin da ke fadin kasar.

Shugaban kungiyar Gbenga Adebayo ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran kungiyar Damian Udeh ya fitar a ranar Laraba.

Masu anfanin da wayoyin hannu a Nijeriya dai na kokawa da wahalar da suke fuskanta wajen dawo da layukansu da suka lalace ko suka bace.

Sai dai kuma Kungiyar ta ce, ta ankara da kalubalen da jama’a ke fuskanta wajen dawo da layukan nasu tun bayan dakatarda sayarwa da kuma rajistar layuka a kasar.

Kungiyar ta kuma ba jama’a tabbacin kamfanonin na yin aiki tare da hukumar bada shaidar zama dan kasa wajen tabbatar da ba a samu matsala ba wajen hada lambarsu ta NIN da layukansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply