Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi zargin cewa matan da ke tallar fura da nono na safarar makamai ga ‘yan ta’adda da ke cikin daji, a cewar Daily Trust.
Gwamna Tambuwal ya yi wannan zargin ne a lokacin da ya karbi tawagar shehin malami Dr Ahmad Gummi a Sokoto.
DCL Hausa ta rawaito cewa Tambuwal yace ya kamata mutane su saka lura ga wadanda ke kai kawo cikin gari zuwa daji domin a hana bazuwar makamai da ke tunzura ayyukan ta’addanci.
Gwamnan ya jaddada cewa addinin musulunci, addini ne na zaman lafiya kuma a kodayaushe yana koyar da zaman lafiya da kaunar juna.
