Home Labarai Masu tallar Jaridu sun koka kan rashin ciniki a Sokoto

Masu tallar Jaridu sun koka kan rashin ciniki a Sokoto

18
0

Masu sayar da Jaridu suna kokawa kan matsalolin rashin ciniki da suke fuskanta a wannan lokaci sabanin lokutan baya.

Wasu masu sayar da jaridun na bakin hanya da kuma masu zama kan tebura a Sokoto, da suka bukaci a sakaya sunansu, sun shaida wa DCL Hausa cewa a halin yanzu zama ne kadai suke yi suna dumama tebura amma an daina sayen jaridun sosai don karantawa inda masu sayen suka koma anfani da wayoyin hannu don samun labarai.

A cewar masu sayar da jaridun a can baya, cikin sana’ar suke gudanar da dukkanin harkokin rayuwar su kama daga biyan kudin makarantar yara, hayar gida, da sauran su amma yanzu komai ya tsaya cak.

Suma masu sayen jaridun sun bayyanawa DCL cewa sun mayar da hankali ne ga samun labaran su ta wayoyin hannu sabanin sayen jaridun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply