Home Labarai Masu zamann haya a Kenya sun samu saukin wata biyu

Masu zamann haya a Kenya sun samu saukin wata biyu

58
0

Mazauna gidajen haya a Kenya sun samu garaɓasar zama gidajen hayar kyauta na tsawon watannin Afirilu, Mayu da Yuni saboda ɓarkewar coronavirus a ƙasar.

Ƙungiyar masu bada haya da masu karɓa ta ƙasar LATAK ce ta yi kira ga masu bada hayar a faɗin ƙasar da su bada kyautar ta tsawon watanni huɗu.

Haka kuma sun yi kira ga gwamnatin ƙasar ta bada umarnin dakatar da biyan bashin da masu bada gidajen hayar ke yi a bankunan ƙasar na tsawon watanni 6.

LATAK dai na fatan ganin an ɗauki wannan mataki cikin gaggawa a matsayin wani ɓangare na yaƙi da cutar COVID-19.

Wani mai bayar da haya a yankin Nyandaruwa ne ya fara bada wannan rangwame na watanni biyu ga waɗanda suke haya a gidajen sa wanda hakan ya janyo masa farin jini tare da wasu ƴan ƙasar da suka riƙa koyi da shi.

Tun da farko dai shugaba Uhuru Kenyatta na ƙasar ya yi kira ga masu bada hayar su rage kuɗin hayar wata wata ga ƴan hayar, saboda matsalolin kuɗin da aka shiga.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply