Home Labarai Masu zanga-zangar EndSARS sun cinna wuta gidan mahaifiyar gwamnan Lagos

Masu zanga-zangar EndSARS sun cinna wuta gidan mahaifiyar gwamnan Lagos

140
0

Wasu matasa da ke zanga-zanga a birnin Lagos sun cinna wuta a gidan da mahaifiyar gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu take zaune.

Punch ta labarta cewa kafin banka wuta a gidan, sai da matasan suka fara jefe-jefen duwatsu cikin gidan.

Dama dai gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya saka dokar hana fita domin kawo karshen zanga-zangar EndSARS.

Wani shaidar gani da ido ya fada wa manema labarai cewa daya daga cikin matasan na rike da jarkar fetur ya nemi kutsa kai cikin gidan, amma aka hana shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply