Home Labarai Masu zanga-zangar EndSARS sun kashe ‘yansanda 22 da kona ofisoshin ‘yansanda 205...

Masu zanga-zangar EndSARS sun kashe ‘yansanda 22 da kona ofisoshin ‘yansanda 205 – IGP

114
0

Babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Muhammad Adamu ya tabbatar da cewa ‘yansandan kasar sun gudanar da aikinsu bisa kwarewa a lokacin zanga-zangar EndSARS a wasu sassan kasar.

Muhammad Adamu ya yi wannan la’akarin ne biyo bayan wani rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar cewa ‘yansanda sun harbi masu zanga-zangar lumana.

A cikin wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta kasa Frank Mba, ta ce wannan rahoto na Amnesty babu kanshin gaskiya a cikinsa, ya ma yi hannun riga da ainihin abin da ya faru.

Ya ce akwai rahoto da ke nuna cewa an yi wa ‘yansanda 22 kisan gilla, tare da kone ofisoshin ‘yansanda kurmus 205 ciki ha da gine-ginen kamfuna da na gwamnati.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply