Home Labarai Masunta sun zama muloniyoyi a jihar Kebbi

Masunta sun zama muloniyoyi a jihar Kebbi

63
0

A ranar Asabar ne aka kammala bikin kamun kifi na Argungu da ke jihar Kebbi.

A wajen wannan taro dai Abubakar Ya’u daga ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi ya zo na ɗaya da ya kamo kifi mai nauyin 78kg.

Haka ma Bala Yahaya Bagaye daga Augie ya zo na biyu da kifi mai nauyin 75kg sai kuma Maiwake Sani Silame daga jihar Sokoto ya zo na uku da kifi mai nauyin 70kg.

An cancare masuntan dai da miliyoyin kuɗi, motoci da kujerun Makka daga ɓangarorin gwamnati, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane.

Abubakar Ya’u da ya zo na ɗaya ya samu jimillar kuɗin da suka kai Naira miliyan 10, motoci biyu da kujerar Makka biyu.

Daga cikin waɗanda suka bada kyautukan akwai ƙungiyar gwamnoni Arewa da ta bada ₦3m ga na ɗaya, ₦2m ga na biyu ₦1m ga na uku.

Haka shima Aminu Tambuwal ya bada adadin waɗannan kuɗaɗe ga zakarun, saidai ya ƙara da kujerar Makka ga na uku, wanda ya fito daga jihar sa ta Sokoto.

Da yake magana a wajen taron, shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana taron a matsayin wata alama da ke nuna yadda Allah ya albarkaci Nijeriya da al’adu daban-daban.

Shima gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya bayyana taron a matsayin abun tarihi da ya cancanci nuna farin ciki da zuwan shi ba wai ga jama’ar jihar kaɗai ba, har ma nijeri3baki ɗaya.

A jawabin sa na maraba tun da farko, mai martaba sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya godewa shugaba Buhari kan ƙoƙarin da yake na samar da zaman lafiya a ƙasar wanda har ya kai ga har an dawo da wannan biki mai ɗunbin tarihi da ak dakatar sama da shekaru goma da suka wuce.

Haka kuma sarkin ya godewa dukkan waɗanda suka taimaka ganin an aiwatar da bikin cikin nasara, tun daga kan gwamnatin jihar, masarautu, kamfanoni, dama waɗanda suka halarci taron.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply