Home Sabon Labari Matafiya sun yi cirko-cirko a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Matafiya sun yi cirko-cirko a hanyar Kaduna zuwa Abuja

75
0

Samuel Aruwan kwamishinan harkokin tsaro a jihar Kaduna ya wallafa cewa gwamnati ta samu labarin cunkoson motoci da ya hana masu motoci wucewa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce tuni gwamnati ta fara kokarin shawo kan lamarin. A rubutun da yayi a shafinsa na fezbuk ya ce za a magance matsalar a cikin kankanin lokaci.

Samuel Aruwan kwamishinan harkokin tsaro a jihar Kaduna

Sai dai Mr. Aruwan bai bayyana ko mene ne dalilin cirko-cirkon da masu mota suka yi ba. Amma ya ce cunkosan motocin yafi yawa a wurin kamfanin Olam idan ka kusa shigo wa Kaduna daga Abuja.

Hanyar Kaduna zuwa Abuja a baya bayan nan ta zama abin tsoro, inda kidinafas kan yiwa matafiya kofar rago duk da jamian tsaron da gwamnati ta jibge.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply