Home Coronavirus Mataimakin gwamnan Bauchi ya kamu da corona

Mataimakin gwamnan Bauchi ya kamu da corona

107
0

Gwamnatim jihar Bauchi ta sanar da cewa shugaban kwamitin yaki da corona kuma mataimakin gwamnan jihar Sen. Baba Tela ya kamu da cutar corona.

Tabbatar da cewa ya harbu da cutar ya biyo bayan gwajin da hukumar NCDC ta yi masa kan cutar.

A wata takarda daga fadar gwamnatin jihar Bauchi mai dauke da sa hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan Mukhtar Gidado ta ce yanzu haka mataimakin gwamnan ya killace kansa.

Bugu da kari takardar ta ce an dauki samfurin makusantansa domin yi musu gwaji don gano hakikanin matsayar lafiyarsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply