Matan nan 4, tsoffin ma’aikatan otal din Signatious da ke Warri jihar Delta, sun nemi diyyar Naira bilyan 1 daga wajen mamallakin otal din Mr Kenneth Gbagi tare kuma da neman yafiya.
Rahotanni sun Mr Kenneth wanda tsohon karamin ministan ilmi ne a Nijeriya ne, ya sa an yi wa matan tsirara bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Tawagar lauyoyin matan, karkashin jagorancin Mr Kunle Edun, sun mika bukatarsu ne a ranar Larabar nan, 23, ga Satumba, 2020 a cikin wata takarda da suka aike da ita ga Mr Kenneth.
Takardar mai taken “yadda aka ci zarafinmu a otal din Signatious” ta yi takaicin yadda ake cin zarafin dan’Adam musamman ma mata.
