Home Labarai Matan Kannywood sun fara fallasa asirin juna

Matan Kannywood sun fara fallasa asirin juna

390
0

Tun bayan bayyanar hotunan nuna tsiraici na jarumar Hausa Fim Rahama Sadau a kafafen sadarwa na zamani, maganganu da gutsiri-tsoma suka cigaba da wakana a tsakanin jarumai mata na Kannywood na fallasa asirin juna.

Tsohuwar Jarumar masana’antar Hafsat Shehu ta fito a wani faifan bidiyo tana kuka gami da la’antar Rahama Sadau wadda ta bayyanata a matsayin Shaiɗaniya.

Jarumai irin su Rashida Mai Sa’a da Fati Washa, su ma ba a bar su a baya ba wajen sukar lamirin shigar baɗala da sanannniyar jarumar ‘yar asalin garin Kaduna ta yi.

Jaridar “Muryar ‘Yanci” ta ba da rahoton cewa bayan faruwar hakan ne tsohuwar jaruma Mansura Isah ta bayyana a wani bidiyo tana sukar jaruman da ke surutu akan shigar ta Rahama Sadau ta yi a hotunan.

Da alamun kalaman Mansura Isah sun fusata wata jarumar wacce aka fi sani da Fati Slow-motion, inda ta fito ta mayar da martani ga Mansura Isa a kan fallasar da ta yi wa ‘yan matan Kannywood da suka caccaki Rahama Sadau kan shigar da ta yi.

Fati ta gargadi Mansura a kan ta kiyaye ta don kada ta bari su yi tone-tone, idan ba haka ba sai ta kwance mata zani a kasuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply