Home Kasashen Ketare Matar Charles Taylor ta koma Liberia bayan kotu ta wanketa daga laifukan...

Matar Charles Taylor ta koma Liberia bayan kotu ta wanketa daga laifukan yaki

150
0

Matar tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor, Agnes Reeves-Taylor ta sake komawa kasar, bayan wata kotu a kasar Birtaniya ta yi watsi da karar da aka shigar a kanta watanni bakwai da suka wuce kan laifukan yaki.

A shekarar 2017 ne aka gurfanar da ita kan wasu zarge-zarge da suka hada da sanya yara cikin yaki, a lokacin yakin basasar kasar da ke yammacin Afirka, wadda ta karyata zargin.

Yanzu haka dai, tsohon mijinta na zaman gidan yari a kasar Saliyo, kan hukuncin daurin rai-da-rai da aka yanke masa saboda aikata laifukan yaki.

Magoya bayan jam’iyyar Taylor ta NPP na nuna farin cikinsu da dawowarta Liberiya a shafukan sada zumunta.

Har yanzu dai ana daukarta a matsayin uwar tsohuwar jam’iyyar mai mulki, saidai har yanzu babu tabbaci ko uwar gida Taylor, wadda tsohuwar malamar jami’a ce, za ta shiga harkokin siyasar kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply