Yahaya Maiyaki dan jarida wanda yanzu haka yake jihar Sokoto a matsayin ma’aikacin rediyo Nijeriya Kaduna ya musanta cewa shi ne matarsa ta dabawa wuka a ciki.
A ranar Asabar labari ya cike garin Kaduna ciki har da wasu gidajen rediyo da suka yada cewa matar Yahaya Maiyaki ta yanke shi a cikinsa biyo bayan wata sa-in-sa da suka yi a gidansu da ke layin Sardauna Crescent a birnin Kaduna.
Sai dai kuma jimkadan bayan da labarin ya fara bazuwa sai dan jaridar ya hau shafinsa na fezbuk, inda ya ce shi a yanzu haka ma ya na Sokoto amma kwatsam sai ya ji mutane suka kira shi suna masa jaje.
Ya ce a zahirin gaske wani Dan uwansa da ke da suna irin nasa wanda ke da inkiya da Dan Asabe shi ne wannan jarrabawa ta fadawa.
Tun kuma a jiya rahotanni sun ce yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin har ma sun kama ita matar da ake zargin ta yi wannan aiki mara kyau.
