Home Labarai Matasa dubu 500 za su samu horon fasahar sarrafa na’urar kwamfuta

Matasa dubu 500 za su samu horon fasahar sarrafa na’urar kwamfuta

78
0

Ma’aikatar matasa da raya al’adun gargajiya da ma wasanni ta Nijeriya ta bayyana cewa za ta kara fadada shirin koyar da fasahar zamani ta yadda akalla matasa dubu 500 za su amfana da shirin a fadin kasar nan.

Ministan matasa da wassanni na Nijeriya Mr Sunday Dare ne ya shaida haka ga manema labarai a Abuja

Ya ce ma’aikatar za ta yi amfani da tallafin annobar corona da aka ba ma’aikatu domin aiwatar da wannan shiri.

Mr Dare ya kara da cewa ma’aikatar za ta horas da matasan yadda za su iya gyara da kuma sarrafa na’urar kwamfuta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply