Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Matasa masu yi wa ƙasa hidima za su samu aikin SDGs

Matasa masu yi wa ƙasa hidima za su samu aikin SDGs

172
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Nijeriya za ta ɗauki matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), tare da jakadun ɗorewar manufofin inganta rayuwar al’umma na wannan ƙarnin aiki, domin tafiyar da shirin kyautata rayuwar al’umma na tsawon shekaru goma a matakin yankunan karkara.

Lokacin da shugaba Buhari ke halartar taron na SDGs

 

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayi da ake gudanar da taron shirin kai tsaye ta kafar intanet, wanda babban Sakataren majalisar dinkin Duniya António Guterres ya jagoranta karo na 75.

Buhari ya yi bayani akan tsare-tsaren da suka fito da manufar Nijeriya kan yaƙar talauci da tabbatar da ci gaban tattalin arziƙi.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na aiwatar da manufofin inganta rayuwar al’umma na tsawon shekaru 10.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply