Home Lafiya Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar aure a Sokoto

Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan tsadar aure a Sokoto

290
0

Ɗaruruwan matasa a jihar Sakkwato sun gudanar da wani tattaki na nuna rashin jin daɗinsu kan matsalar tsadar aure a jihar.

Matasan dai ɗauke da kwalaye masu nuni da cewa ya kamata hukumomi su soke kayan an gani ana so da ake kashe maƙudan kuɗi wajen haɗa su.

Wannan matsala dai na ciwa matasa da dama tuwo a ƙwarya musamman ma ‘ƴan Rabbana ka wadata mu.

Matasan dai sun sha yin kiraye-kirayen a soke waɗannan kaya, amma yin ko oho da hukumomi suka yi shi ne ya kai ga ɗaukar matakin yin zanga-zangar a cewar Ibrahim, wani matashi dake cikin masu tattakin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply