Home Siyasa Matasan Arewa sun nemi Fulanin dake Kuda da su dawo gida

Matasan Arewa sun nemi Fulanin dake Kuda da su dawo gida

124
0

Muzgunawa Fulani A Kudu: MATASAN AREWACIN NAJERIYA SUN BA FULANI SHAWARA SU DAWO GIDA.

Abdul Aziz Sulaiman mai magana da yawun kungiyar Coalition of Northern Groups ya ce sun zauna da kungiyar Northern Elders Forum a ranar Talata inda suka yadda cewa ana ci gaba da muzgunawa Fulani makiyaya a jihohin kudancin kasar nan.

A don haka ne Abdul Aziz yace kungiyar su na kira ga duk wani bafullatani makiyayi da rayuwar shi ke cikin hadari a kudu da ya dawo Arewacin Najeriya don ya samu zaman lafiya da tsaron rayuwarsa.

Zargin fulani a matsayin masu aikata laifi na ci gaba da kamari a kudancin Najeriya tun bayan da kungiyar Afenifere ta yarbawa ta zargi fulani da kisan yarinyar shugaban kungiyar a jumaar da ta gabata.

Ya kuke kallon wannan shawara?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply