Home Coronavirus Matasan NYSC 8 sun kamu da corona

Matasan NYSC 8 sun kamu da corona

129
0

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar cewa ta gano matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC 8 da aka tura jihar na dauke da cutar corona.

Babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Salisu Mu’azu Babura a taron manema labarai a birnin Dutse.

Yace daga cikin mutane 15 da aka yi wa gwajin cutar ne aka samu 8, kuma yanzu haka su na amsar magani a cibiyoyin killace masu dauke da cutar.

Salisu Babura yace gwamnatin jihar ba ta da wani tsari na sake kakaba dokar kulle ta “lockdown” sai dai idan mutane sun ki bin dokokin da aka gindaya na kauce wa kamuwa ko yada cutar.

Babban sakataren yace gwamnatin jihar za ta kuma bude karin cibiyoyin killace masu dauke da cutar a Birnin Kudu da Jahun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply