Home Labarai Matashi ya kashe kan shi saboda budurwa a Kano

Matashi ya kashe kan shi saboda budurwa a Kano

241
0

Wani matashi a jihar Kano da aka bayyana sunan shi da Ashiru Musa Danrimi, mazauni Kadawa a karamar hukumar Ungogo mai kimanin shekaru 25 ya kashe kansa ta hanyar caka wa cikinsa wuka sakamakon jin labarin budurwarsa wacce suka dade suna soyayya mai suna Ummi Muhammad za ta angonce da wani.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce jami’an ‘yan sanda ne suka garzaya da wannan matashi zuwa asibitin kwararru na Murtala da ke Kano inda aka tabbatar masu da cewa tuni rai ya yi halinsa.

Sai dai tuni Kwamashinan ‘yan sanda na jihar ta Kano CP Habu Sani, ya umurci da a gudanar bincike mai zurfi kuma gamsasshe akan faruwar wannan al’amarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply