Home Kasashen Ketare Matashin ɗan Nijeriya ya fito takarar gwamna a Amirka

Matashin ɗan Nijeriya ya fito takarar gwamna a Amirka

196
0

Wani ɗan Nijeriya mai shekara 34 Austin Chenge ya fito takarar gwamnan jihar Michigan ta Amirka, a zaɓen da za a gudanar ƙasar na shekarar 2022.

Wata sanarwa da ta fito daga shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar kula da ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje Abdul-Rahman Balogun, ya ce Chenge, ɗan asalin jihar Benue zai fafata ne da Lamar Smith a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Republican.

Sanarwar ta ce Chenge ya ayyana ƙudirinsa na tsaya wa takarar ne a watan Maris, 2020, wanda ya sanya ya zama ɗan jam’iyyar Republican na farko da ya yi hakan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply