Home Labarai Matashin da ya karbi milyan 2 bayan ya yi garkuwa da mahaifinsa

Matashin da ya karbi milyan 2 bayan ya yi garkuwa da mahaifinsa

63
0

‘Yansanda a Nijeriya sun ce sun cafke wani matashi dan kimanin shekaru 20, mai suna Abubakar Amodu, da ya hada kai da wata kungiyar’ yan daba suka sace mahaifinsa tare da karbar kudin fansa har Naira miliyan 2.

Matashin na daya daga cikin mutane 25 da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, ta kasa CP Frank Mba ya gabatar daga cikin wadanda aka yi holensu a harabar rundunar bisa samunsu da aikata laifuka daban-daban a Abuja.

An dai kama wanda ake zargin, tare da sauran abokanan nasa da ake zargin sun aikata wannan ta’asa, inda ya bayyana wa rundunar ‘yansandan cewa, shi yana aiki tare da mahaifinsa a gona domin taya shi kiwon shanu.

Daga bisani sai mahaifin nasa ya ‘yanta shi da shanu 15 domin ya bar gida ya tafi ya kiwata su.

Yace ya yi abokantaka da mambobin kungiyar, wadanda suka fada masa cewa mahaifinsa mai kudi ne, kuma ya kamata a sace shi don neman kudi.

Amodu ya aminta kuma ya shirya masu yadda za su yi don yin nasarar satar mahaifinsa.

Rahotanni sun ce bayan mutanen sun sami nasarar sace mahaifin na Amodu daga baya ya sun ba shi N200,000 a matsayin kasonsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply