Home Labarai Matashin da ya kashe wanda ke soyayya da tsohuwar matarsa a Jigawa

Matashin da ya kashe wanda ke soyayya da tsohuwar matarsa a Jigawa

221
0
Ankwa mai laifi
Ankwa mai laifi

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa, ta ce ta baza jami’anta domin su yi farautar wani matashi, da aka bayyana sunansa da Umaru bisa zargin sa da kashe wani mutum mai shekaru 45 da ya ke zarginsa da yin soyayya da tsohuwar matarsa.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdu Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace matashin da da ake zargi, ya aikata kisan ne a ranar Litinin ta makon nan.

Jinjiri ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Dakaiyawa da ke cikin karamar hukumar Kaugama ta jihar.

Ya ce “A ranar 9 ga Nuwamban nan ne da misalin karfe 3 na yamma aka kai rahoto ofishin ’yansanda da ke kauyen Dakaiyawa cewa wani matashi da ba a bayyana cikkaken adireshinsa ba, ya daba wa wani mutum mai suna Sale Dange dan shekara 45, wuka inda ya yi sanadiyar halaka shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply