Home Labarai Matashin da ya samu kyautar ₦10,000 bayan ya tura wa Rarara dubu...

Matashin da ya samu kyautar ₦10,000 bayan ya tura wa Rarara dubu 1

493
0

Wani matashi mai suna Sani Yusuf Nababa (Mafeous) da ke garin Daura a jihar katsina, ya sami kyautar Naira dubu 10 bayan ya tura wa mawaki Dauda Kahutu Rarara Naira dubun da ya bukata a wajen duk wani masoyin shugaba Buhari domin ya saki sabuwar wakar da ya rera masa.

Sani Yusuf ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, tare da nuna shaidar shigar kudin asusun shi da ya ke ajiya a banki.

“Allah mai iko jiya da dare wani ya kirani a waya yace kai ne wanda ka ba da gudunmawar 1g ga Rarara?

Nace masa eh nine, sai yace mani in tura masa Acc dina sabida yace mani zan maida maka kudin ka Nace masa Aa wlh ni nayi nayi nabada bani so.

Anan take yace shi ma so yake ya bani wani abu kyauta albarkacin Ni masoyin Buhari ne nace masa ok to kamar wasa, Yanzun nan naji alert na 10k sun shiga.” Inji Sani Yusuf

Sai dai, shi ma Sani ya bayyana cewa wannan dubu goma da ya samu daga bawan Allah nan, ba zai kashe ta ba, zai yi wani abu na alkhairi da wadannan kudade.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply