Ministar kuɗi da tsare-tsare ta Nijeriya ta ce ba lallai ba ne matatar man Ɗangote ta rage farashin mai idan ta fara aiki a baɗi ba, domin za ta yi amfani ne da farashin duniya.
Ministar wadda ta bayyana haka a wani shiri na NTA, ta ce hakan zai faru ne saboda an samar da matatar ne a yankin fitar da kayayyaki ƙasashen waje, da ke Lagos.
Ministar ta ce abun da kawai Nijeriya ba za ta biya ba shi ne, kuɗin dakon man, amma farashin man zai kasance ɗaya ne da na duniya.
