DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeBabban Labari Matatun man fetur na Nijeriya za su dawo aiki gadan-gadan - Tinubu

Matatun man fetur na Nijeriya za su dawo aiki gadan-gadan – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ma’aikatan masana’antar man fetur cewa matatun man Nijeriya da suka shafe shekaru ba sa aiki yadda ya kamata, za su dawo da aiki gadan-gadan.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi shugabannin ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (NUPENG) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ƙasar ya ce kasancewar wuta ko hayaƙi yana tashi daga matatar mai ba yana nufin matatar tana aiki yadda ya kamata ba, yana mai cewa dole ne matatun su kasance masu samar da riba tare da cika manufar da aka gina su.

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito Shugaba Tinubu ya ce ya ɗauki alhakin gyara kadarorin ƙasar da kuma matsalolin da gwamnatocin baya suka bari, yana mai cewa ba zai yi amfani da abin da ya gada a matsayin uzuri ba.

Tinubu ya ce biyan albashi a kan lokaci ga ma’aikatan gwamnati a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi na taimakawa wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci da kuma rage matsin tattalin arziki ga iyalai.

Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta samu kuɗaɗen gudanar da wasu manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da manyan titunan Lagos zuwa Ibadan, Abuja zuwa Kaduna, Abuja–Kano da Sokoto–Badagry.

Ya kuma bukaci NUPENG da ta taimaka wajen ganin alfanun amfani da iskar gas ɗin CNG sun isa ga masu amfani da sufuri, yana mai cewa fa’idodin shirin ba su yaɗu cikin sauri kamar yadda yake fata ba.

A nasa jawabin, shugaban NUPENG, Salimon Oladiti, ya koka kan yadda ake ci gaba da ɗaukar ma’aikata na ɗan lokaci a ɓangaren hako mai da iskar gas, duk da tattaunawar da aka yi da wasu kamfanoni.

Oladiti ya ce NUPENG da PENGASSAN sun guji ɗaukar matakin yajin aiki saboda fargabar illar da hakan ka iya haifarwa ga tattalin arzikin ƙasa, inda ya roƙi Tinubu da ya sa baki domin kawo ƙarshen lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata