Iyaye mata a jihar Jigawa, sun zargi mazajensu da ba da gudunmuwa wajen tilasta tura ‘ya’yansu mata talla.
Wata uwa, ta shaida wa Freedom Radio cewa mazajen ne suke gaza sauke nauyin da ya rataya kansu.
Ta ce “abin da ya sa muke dora musu talla, saboda maza sun gaza sauke nauyin da Allah ya dora musu, sun sakar mana, don haka ya zama dole mu nemi mafita” a cewar ta.
Ita kuwa, wata uwar cewa ta yi “ai talla ta zama dole domin ta haka ne muke rufa wa kanmu asiriva lamurranmu na yau da kullum”.
Mafi yawa dai, ana samun rahotannin cin zarafin ‘ya’ya mata musamman ta dalilin talla, ba ya illar rashin zuwa makaranta domin neman ilmin addini da na boko.
