Mazauna ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja sun fara barin gidajensu zuwa Jamhuriyar Benin domin neman tsira daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankin.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ɗan takarar jam’iyyar ADC na majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Borgu/Agwara, Murtala Haliru Dantoro, ne ya bayyana hakan, yana mai kira ga Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin tarayya da su gaggauta tura rundunar tsaro da za ta kare yankin.
Dantoro ya bayyana damuwar ne yayin wani taron manema labarai, inda ya ce matsalar tsaro a masarautar Borgu na ƙara ta’azzara, yayin da ake hallaka mutane, garkuwa da mutane, raba jama’a da muhallansu da kuma takaita ayyukan noma da zirga-zirga ke ci gaba da addabar al’umma.
Ya ce mazauna yankin ba sa neman gwamnati ta jira sai an kai hari sannan ta zo ta ceto su, suna bukatar matakan tsaro na dakile hare-haren tun kafin su faru.
Ya jaddada cewa abin da al’ummar Borgu ke nema shi ne kariyar da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar wa kowane ɗan Nijeriya.
Dan takarar na ADC ya kuma bayyana damuwa kan lalacewar wata babbar gada da ke haɗa Borgu da Jamhuriyar Benin, da kuma jihohin Kebbi da Sokoto, yana mai cewa lalacewar gadar ta kawo cikas ga zirga-zirga, kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki a yankin.
Dantoro ya ce haɗuwar matsalar tsaro da lalacewar muhimman hanyoyin sufuri na ƙara jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali, inda wasu daga cikinsu ke tilasta barin Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin neman mafaka.
Ya bayyana lamarin a matsayin matsalar jin kai da kuma barazana ga tsaron ƙasa, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta Jihar Neja da su ɗauki matakin gaggawa kafin ƙarin mutane su rasa muhallansu.
Haka kuma, ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji na cikin gida da na ƙasa da ƙasa da su taimaka wa waɗanda rikicin ya raba da muhallansu, musamman mata da yara, ta hanyar samar musu da matsuguni, abinci da kiwon lafiya.
