DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeWasanniMbappe da Tchouameni sun dawo atisayen Real Madrid gabanin El Clasico

Mbappe da Tchouameni sun dawo atisayen Real Madrid gabanin El Clasico

Tauraron ɗan wasan gaba na Real Madrid, Kylian Mbappe, ya dawo atisaye bayan ya murmure daga raunin da ya hana shi buga wasa na tsawon makonni biyu, gabanin fafatawar El Clasico da Barcelona.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa Mbappe ya shiga wani ɓangare na atisayen ƙungiyar ranar Juma’a, kwanaki biyu kafin wasan da Real Madrid za ta je ta buga a filin Barcelona.

Haka kuma ɗan wasan tsakiya, Aurelien Tchouameni, ya shiga atisayen bayan rikicin da ya faru tsakaninsa da abokin wasansa Federico Valverde, wanda rahotanni suka ce har sai da aka yi masa ɗinki bayan hatsaniyar.

Real Madrid ta tabbatar da buɗe bincike kan ’yan wasan biyu bayan rikicin da ya faru a filin atisaye, wanda ya kasance ɗaya daga cikin rikice-rikicen da suka addabi ƙungiyar a baya-bayan nan.

Rahotanni sun nuna cewa akwai matsin lamba a cikin ƙungiyar Real Madrid yayin da take fuskantar yiwuwar kammala kakar wasa ba tare da lashe babban kofi ba a karo na biyu a jere.

Barcelona dai na gaba da maki 11 a teburin La Liga, kuma tana buƙatar canjaras kawai a wasan El Clasico domin tabbatar da lashe gasar Sifaniya karo na gaba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata