Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan Afirka, sun yi tir da gwamnatin Mali, kan abun da suka kira yin amfani da jami’an tsaro kan masu zanga-zanagar neman shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus.
Zanga-zanar, wadda aka faro a watan jiya ta rikide zuwa rikic a ranar Juma’a, lokacin da ‘yan sanda suka budewa masu zanga-zanagar wuta, wadanda wasu daga cikin su sun mamaye gine-ginen gwamnati a birnin Bamako na kasar.
A cikin wata sanarwa da ofishin MDD a Mali, kungiyar AU, kungiyar tarayyar Turai da kuma ECOWAS suka fitar, dukkan su, sun soki hukumomin na Mali kan abunda suka yiwa ‘yan zanga-zangar.
Sun kuma yi tir da lalata kayan gwamnati da masu zanga-zangar suka yi, tare da kiran su, da su sanya dattaku.
