Home Kasashen Ketare Messi zai ci gaba da zama a Barcelona

Messi zai ci gaba da zama a Barcelona

196
0

Shahararren dan wasan tawagar Barcelona Lionel Messi ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a kungiyarsa saboda zai yi wuya matuka kungiyoyin da ke son daukar sa su iya biyan kudin da Barcelona za ta sake shi, kuma ba ya son su yi rabuwar ‘yan bori da kulob din.

A makon jiya ne dai Lionel Messi ya bayyana cewa yana son raba gari da Barcelona, sakamakon mawuyacin halin da kungiyar ke ci gaba da samun kanta game da harkokin wasanni.

Messi ya ce babu yadda zai yi, zai ci gaba da zama a kungiyarsa saboda shugaban kungiyar ya gaya masa cewa hanyar da zai bi kawai ita ce ta ya biya su Fan miliyan 700 (£ 624m), wanda hakan ba zai yiwu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply