Home Sabon Labari Mikel Obi ya koma Ingila a Stoke City

Mikel Obi ya koma Ingila a Stoke City

132
0

Tsohon ɗan wasan Nijeriya da Chelsea Mikel Obi ya kammala komawarsa Stoke City daga Trabzonspor yana da shekara 33.

A shekarar 2017 ne dai ya Obi ya bar Chelsea zuwa Tianjin Teda, kuma bayan nan ya dawo Middlesbrough kafin ya tafi Trabzonspor yanzu kuma ya sake dawo wa Ingila a ƙungiyar Stoke da take kakar firimiya ta biyu watau Championship.

Stoke City ce ta bayyana ɗauko ɗan wasan a shafinta na intanet da twitter bayan ɗan wasan tsakiyar ya kammala sa hannun kasancewa a ƙungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply