Home Kasashen Ketare Miliyoyin masu zabe na kokarin zaben shugaban kasa a cikin ‘yan takara...

Miliyoyin masu zabe na kokarin zaben shugaban kasa a cikin ‘yan takara 29 a Nijar

173
0

A wannan Lahadi 27 ga wannan wata na Disemba ne ake bude runfunan zaben ‘yan majalisar dokoki da na shugaban kasa zagayen farko a fadin kasar jamhuriyar Nijar. A jimilce kimanin mutane miliyan bakwai da dubu dari hudu da ‘yan kai ne ake sa ran za su fito domin halartar runfunan zaben a cikin kasar kuma ‘yan takara 29 ne ke fafatawa a neman kujerar shugabancin kasar.

A baya dai ‘yan takara 30 da za su fafata sai dai daga bisa shugaban jam’iyyar UDR Tabbat Amadou Cissé ya janye takarar shi domin mara wa dan takarar jam’iyyar RDR Tchanji Mahaman Ousman baya

A zaben da ya gabata na kananan hukumomi dai an samu fitar akalla mutane miliyan shida da suka halarci runfunan zaben adadin kuma da ya kai na kaso 85 cikin na adadin wadanda aka yi wa rajistar cancantar kada kuri’a

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply