Home Labarai Mine ne gaskiyar labarin soyayyar Hamisu Breaker da Fatima Ali Nuhu? 

Mine ne gaskiyar labarin soyayyar Hamisu Breaker da Fatima Ali Nuhu? 

298
0

Shahararren mawakin soyayyar nan dan asalin jihar kano Hamisu Breaker Doroyi ya ce ko kadan babu kamshin gaskiya dangane da yadda jama’a ke yamadidi da shi cewa yana soyayya da ƴar gidan jarumi Ali Nuhu wato Fatima Ali Nuhu.

Breaker ya yi wannan bayanin ne a yayin da yake amsa tambayoyin al’umma a shagalin wani biki da aka gayyace shi.

Breaker ya ce “Na sha gani a YouTube ana sanya bidiyon akwatinan kayan lefe ana cewa nawa ne da Fatima Ali Nuhu.

“Wallahi duk labari ne, ni rabon da naga Fatima Ali Nuhu tun tana ƴar karama, kawai mutane ne ke hada irin wadannan abubuwa a shafinsu na YouTube domin su samu kudi da ma yawan mabiya a shafikansu” inji Hamisu Breaker.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply