Home Sabon Labari Ministan Sadarwa ya fara aiki, ya tura wa ma’aikata wani muhimmin gargadi

Ministan Sadarwa ya fara aiki, ya tura wa ma’aikata wani muhimmin gargadi

86
4

Abdullahi Garba Jani 

Sabon ministan sadarwa na Nijeriya Dr Isah Ali Pantami ya hori ma’aikatan ma’aikatar sadarwa ta Nijeriya da su ci gaba da gudanar da aiki ba kasala sannan su guji nuna kabilanci.

Dr. Isah Pantami ya yi wannan jan kunnen ne a lokacin da ya ke jawabi ga mahukunta da sauran ma’aikatan ma’aikatar a lokacin da ya kama aiki a ranar Larabar nan, bayan da shugaba Buhari ya rantsar da su a Abuja.

Ya bukaci ma’aikatan da su hadu don zama tsintsiya daya mai madauri daya don sauke hakkin aikin da ya rataya kansu.

Ministan ya kuma sha alwashin karfafa guiwa ga hukumomin da ke karkashin ma’aikatar don su gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

Sai Dr. Pantami yace za a shirya wani taron horaswa ga ma’aikatan na kwanaki 2 don tattauna batutuwa da lalubo bakin zaren warware kalubalen da ma’aikatan da ma’aikatar ke fuskanta.

Babban sakatare na ma’aikatar, Mr. Istifanus Fuktu, ya bukaci sabon ministan da ya yi damara mai kwari don tunkarar kalubalen da suka yi wa ma’aikatar katutu.

Sai ya yi kira ga ma’aikatan da su kasance masu bin doka da oda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

4 COMMENTS

Leave a Reply