Home Labarai Ministan Aikin Gona zai ba cibiyoyin bincike muhimmanci don inganta noma a...

Ministan Aikin Gona zai ba cibiyoyin bincike muhimmanci don inganta noma a Nijeriya

90
0

Hannatu Mani Abu/dkura

 

Ministan Noma da Raya Karkara Sabo Nanono ya bayyana cewa ma’aikatar aikin noma da kiwo karkashin jagorancinsa za su tabbatar da inganta hukumomin bincike domin samun irin shuka mai inganci.

 

Sabo Nanono ya fadi haka ne a ofishinsa yayin da ya karbar rahoto akan halin da hukumomin binciken aikin noma da ke karkashin ma’aikatarsa ke ciki.

Mohammed Sani Nanono Ministan Aikin Gona na Nijeriya

Ministan ya ce samun irin shuka mai kyau zai taimaka wajen kara yawaitar abincin da ake nomawa a kasar.

 

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in da ke magana da yawun ma’aikatar aikin noma ta Nijeriya Eno Olotu ya ce ministan ya ce “ina so mu mika hankalin mu akan hukumomin bincike ba tare da mun yi wasa da su ba domin su binciko mana irin shuka masu inganci wadanda zasu yi daidai da kasar noman mu.”

 

A makon da ya gabata lokacin da Ministan ya kama aiki ya yi alwashin daukar duk wani mataki da ya dace don inganta sana’ar noma. Ya ce kasashen waje sun zura ido su ga yadda bangaren noma zai kasance. A don haka Ministan ya ce ba za su yi sako-sako ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply