Rahotanni daga Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar nuna cewa ministan kwadago kuma shugaban jam’iyyar PSD Basira Ben Omar ya rasu a wani babban asibitin na birnin Yamai a wannan Lahadi.
Malan Ben Omar dai ya jima yana taka rawa a fannin siyasar jamhuriyyar Nijar ya kuma rike mukammai da dama a fagen siyar kasar.
Mukamin baya bayan nan shine na ministan ilimi mai zurfi da ya rike kafin daga bisani a canja shi da Yahuza Sadisu Madobi
Ya zuwa hada wannan rahoto dai babu wani sahinhin dalilin mutuwar tasa a hukumance.
Tuni Shugaban kasar Nijar Muhammadu Yusufu ya miƙa sakon ta’aziyya ga yan’uwa da iyalan mamacin dama yan ƙasa baki daya.
