Wani dan majalisar Wakilai ta tarayya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, kwana daya bayan shugaba Buhari ya bayyana sunansa a cikin wadanda yake son nadawa a matsayin ministoci.
Hon. Emeka Nwajiuba, wanda ya fito daga jihar Imo ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyarsa ta Accord Party zuwa APC a zaman majalisar wakilai na ranar Laraba.
