Home Sabon Labari Muhimman abubuwan da suka faru a gasar firimiya lig a karshen mako

Muhimman abubuwan da suka faru a gasar firimiya lig a karshen mako

70
0

Ahmadu Rabe Yanduna/Jani

Manchester City ta koma ta biyu a kan teburin gasar Firimiya bayan da ta yi nasarar doke Bournemouth da ci 3-1.

Dan wasan city Sergio Aguero ne ya ci kwallo biyu a wasan.

Tottenham kuwa rashin nasara ta yi a gidanta, inda Newcastle United ta yi mata ci daya mai ban haushi 1-0.

Wasan Crystal Palace da Manchester United ya zo da bazata inda Palace din ta lallasa United da ci 2-1 A ranar Asabar. Rabon da Palace ta doke United a Old Trafford tun shekarar 1970 zuwa 71 lokacin gasar ‘yan rukuni na daya.

Wasu yan wasa a firimiya lig ta Ingila

Sauran sakamakon wasannin firimiya lig mako na uku ranar Lahadi:

Bournemouth 1 – 3 Manchester City.

Tottenham 0 – 1 Newcastle United.

Wolverhampton Wanderers 1 – 1 Burnley

Yayin da kulob din Arsenal suka sha kashi a hannun Liverpool da ci 3-1 a filin wasa na Anfield.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply